Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 150 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

1Yabi Ubangiji.Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki;yabe shi a cikin sammai na ikonsa.

2Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;yabe shi saboda mafificin girmansa.

3Yabe shi da ƙarar kakaki,yabe shi da garaya da molo,

4yabe shi da ganga kuna taka rawa,yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

5yabe shi da kuge mai ƙara,yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

6Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.Yabi Ubangiji.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]