Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 149 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

1Yabi Ubangiji.Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,yabonsa a cikin taron tsarkaka.

2Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu;bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.

3Bari su yabi sunansa tare da rawasuna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.

4Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa;yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.

5Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirmasu kuma rera don farin ciki a kan gadajensu.

6Bari yabon Allah yă kasance a bakunansutakobi mai kaifi kuma a hannuwansu,

7don su ɗau fansa a kan al’ummaida kuma hukunci a kan mutane,

8don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi,manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe,

9don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu.Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa.Yabi Ubangiji.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]