Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Isaiah 12 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Waƙoƙin yabo

1A wannan rana za ku ce,“Zan yabe ka, ya Ubangiji.Ko da yake a dā ka yi fushi da ni,amma yanzu ka daina fushi da nika kuwa ta’azantar da ni.

2Tabbatacce Allah shi ne mai cetona;zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba.Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata;ya zama mai cetona.”

3Da farin ciki zan ɗebo ruwadaga rijiyoyin ceto.

4A wannan rana za ku ce,“Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai,a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.

5Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa;bari a sanar da wannan ga dukan duniya.

6Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona,gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]