Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 128 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Waƙar haurawa.

1Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.

2Za ka ci amfanin aikinka;albarku da wadata za su zama naka.

3Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’yaa cikin gidanka;’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitunkewaye da teburinka.

4Ta haka mai albarka yakewanda yake tsoron Ubangiji.

5Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyonadukan kwanakin ranka;bari ka ga wadatar Urushalima,

6bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka.Salama tă kasance tare da Isra’ila.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]