Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 127 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Waƙar haurawa. Ta Solomon.

1In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,masu gininta suna wahala a banza ne.In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,masu tsaro suna yin tsaro a banza.

2Banza ne ka farka da wurika koma da latti,kana fama don abincin da za ka ci,gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.

3’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,yara lada ne daga gare shi.

4Kamar kibiyoyi a hannun jarumihaka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

5Mai albarka ne mutuminda korinsa sun cika da su.Ba za a kunyata su basa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]