Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 126 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Waƙar haurawa.

1Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona,mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.

2Bakunanmu sun cika da dariya,harsunanmu da waƙoƙin farin ciki.Sai ana faɗi a cikin al’ummai,“Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”

3Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu,mun kuwa cika da farin ciki.

4Ka maido da wadatarmu, ya Ubangijikamar rafuffuka a Negeb.

5Waɗanda suka yi shuka da hawayeza su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

6Shi da ya fita yana kuka,riƙe da iri don shuki,zai dawo da waƙoƙin farin ciki,ɗauke da dammuna.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]