Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 125 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Waƙar haurawa.

1Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.

2Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,haka Ubangiji ya kewaye mutanensayanzu da har abada kuma.

3Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasancea kan ƙasar da take rabon adalai ba,domin kada masu adalci su yi amfanida hannuwansu su aikata mugunta.

4Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu,ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.

5Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyiUbangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta.Salama tă kasance tare da Isra’ila.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]