Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 124 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

1Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba,bari Isra’ila yă ce,

2da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu basa’ad da aka auka mana,

3sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu,ai, da sun haɗiye mu da rai;

4da rigyawa ta kwashe mu,da ambaliya ta rufe mu.

5Da ruwa mai haukaya share mu ƙaf.

6Yabo ya tabbata ga Ubangiji,wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.

7Mun tsira kamar tsuntsudaga tarkon mai farauta;an tsinke tarko,muka kuwa tsira.

8Taimakonmu yana a sunan Ubangiji,Wanda ya yi sama da ƙasa.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]