Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 123 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Waƙar haurawa.

1Na tā da idanuna gare ka,gare ka da kursiyinka yake cikin sama.

2Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu,kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta,haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu,sai ya nuna mana jinƙansa.

3Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai,gama mun jimre da reni mai yawa.

4Mun jimre da wulaƙancidaga masu girman kai,reni mai yawa daga masu fariya.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]