Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 122 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

1Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni,“Bari mu tafi gidan Ubangiji.”

2Ƙafafunmu suna tsayea ƙofofinki, ya Urushalima.

3An gina Urushalima kamar birninda aka yi a harhaɗe wuri guda.

4A can ne kabilu suke haurawa,kabilan Ubangiji,don su yabi sunan Ubangijibisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.

5A can kursiyoyin shari’a yake tsaye,kursiyoyin gidan Dawuda.

6Ku yi addu’a don salamar Urushalima,“Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.

7Bari salama ta kasance a katangarkizaman lafiya kuma a fadodinki.”

8Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina,zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”

9Saboda gidan Ubangiji Allahnmu,zan nemi wadatarki.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]