Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 129 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Waƙar haurawa.

1Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami,bari Isra’ila yă ce,

2sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami,amma ba su yi nasara a kaina ba.

3Manoma sun nome bayanasuka yi kunyoyinsu da tsayi.

4Amma Ubangiji mai adalci ne;ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.

5Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyonaa juye da su baya da kunya.

6Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi,wadda takan bushe kafin tă yi girma;

7da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa,balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.

8Kada masu wuce su ce,“Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku;muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]