Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Job 25 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Bildad

1Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,

2“Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa;yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.

3Za a iya ƙirga rundunarsa?A kan wane ne ba ya haska haskensa?

4Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?

5In har wata da taurariba su da tsarki a idanunsa,

6mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]