Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 23 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Zabura ta Dawuda.

1Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

2Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

3yakan maido da raina.Yakan bi da ni a hanyoyin adalcisaboda sunansa.

4Ko da na yi tafiyata kwari na inuwar mutuwa,ba zan ji tsoron mugu ba,gama kana tare da ni;bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,za su yi mini ta’aziyya.

5Ka shirya mini tebura gaban abokan gābana.Ka shafe kaina da mai;kwaf nawa ya cika har yana zuba.

6Tabbatacce alheri da ƙauna za su bidukan kwanakin raina,zan kuwa zauna a gidan Ubangijihar abada.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]