Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 12 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit. Zabura ta Dawuda.

1Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma;masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.

2Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya;zaƙin bakinsu maganar ƙarya cesuna cike da ruɗu a zukatansu.

3Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsuda kuma kowane harshe mai fariya,

4masu cewa,“Da harsunanmu za mu yi nasara;leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”

5“Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata,zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji.“Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”

6Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure,kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu,aka tsabtacce sau bakwai.

7Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiyaka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.

8Mugaye suna yawo a sakesa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]