Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 13 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

1Har yaushe, ya Ubangiji? Za ka manta da ni har abada ne?Har yaushe za ka ɓoye fuskarka daga gare ni?

2Har yaushe zan yi kokawa da tunaninakuma kowace rana in kasance da damuwa a zuciyata?Har yaushe abokin gābana zai yi nasara a kaina?

3Ka dube ni ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna.Ka ba da haske ga fuskata, ko in yi barci cikin mutuwa;

4abokin gābana zai ce, “Na sha ƙarfinsa,”kuma abokan gābana za su yi murna sa’ad da na fāɗi.

5Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa;zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.

6Zan rera ga Ubangijigama ya yi mini alheri.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]