Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 11 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don busa. Ta Dawuda.

1A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka.Yaya za ku ce mini,“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu.

2Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu;sun kuma ɗana kibiyoyinsudon su harbi mutanen kirki a zuciyadaga cikin duhu.

3Sa’ad da aka tumɓuke tushe,me adali zai iya yi?”

4Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki;Ubangiji yana a kursiyinsa a sama.Yana kallon ’ya’yan mutane;idanunsa suna bincike su.

5Ubangiji yana bincike adalai,amma ransa yana ƙi mugayeda masu son rikici.

6A kan mugaye zai zubagarwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu;iska mai zafi zai zama rabonsu.

7Gama Ubangiji mai adalci ne,yana ƙaunar gaskiyamasu adalci za su ga fuskarsa.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]