Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 4 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda.

1Ka amsa mini sa’ad da na kira gare ka,Ya Allahna mai adalci.Ka ba ni sauƙi daga wahalata;ka ji tausayina ka kuma ji addu’ata.

2Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya?Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya? Sela

3Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa;Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi.

4Cikin fushinku kada ku yi zunubi;sa’ad da kuke kan gadajenku,ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru. Sela

5Ku miƙa hadayun da suka daceku kuma dogara ga Ubangiji.

6Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?”Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.

7Ka cika zuciyata da farin cikisa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.

8Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,gama kai kaɗai, ya Ubangiji,kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]