Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 5 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Busa. Ta Dawuda.

1Ka saurare kalmomina, ya Ubangiji,ka ji ajiyar zuciyata.

2Ka saurare kukata na neman taimako,Sarkina da Allahna,gama gare ka nake addu’a.

3Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata;da safe na gabatar da bukatuna a gabankain kuma jira da sa zuciya.

4Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne;gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta.

5Masu fariya ba za su iya tsayaa gabanka ba.Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.

6Kakan hallaka masu yin ƙarya.Masu kisankai da mutane masu ruɗuUbangiji yana ƙyama.

7Amma ni, ta wurin jinƙanka mai girma,zan shiga gidanka;da bangirma zan durƙusaga haikalinka.

8Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinkasaboda abokan gābana,ka fayyace hanyarka a gabana.

9Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita;marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu.Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne;da harshensu suna faɗin ƙarya.

10Ka furta su masu laifi, ya Allah!Bari makircinsu yă zama fāɗuwarsu.Ka kore su saboda yawan zunubansu,saboda sun tayar maka.

11Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna;bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki.Ka buɗe kāriyarka a bisansu,domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.

12Gama tabbatacce, ya Ubangiji, kakan albarkaci adalai;kakan kewaye su da tagomashinka kamar garkuwa.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]