Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 3 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom.

1Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne!Su nawa suke gāba da ni!

2Da yawa suna magana a kaina suna cewa,“Allah ba zai cece shi ba.” Sela

3Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

4Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

5Na kwanta na yi barci;na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

6Ba zan ji tsoro ko dubu gomasuka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

7Ka tashi Ya Ubangiji!Ka cece ni, ya Allahna!Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi;ka kakkarya haƙoran mugaye.

8Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo.Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]