Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 15 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Zabura ta Dawuda.

1Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka?Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?

2Sai wanda ba shi da laifikuma yana yin abin da yake daidai,wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa

3ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa,wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa muguntaba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,

4wanda yake ƙin mugun mutumamma yakan girmama masu tsoron Ubangiji,yakan cika alkawarinsako da ma ya zafe shi,

5wanda yake ba da rance ba tare da ruwa bakuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi.Shi wanda yake yin waɗannan abubuwaba zai taɓa jijjiguwa ba.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]