Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 16 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Miktam ne na Dawuda.

1Ka kiyaye ni, ya Allah,gama a cikinka nake samun mafaka.

2Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana;in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”

3Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa,su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana.

4Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli.Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini bako in ambaci sunayensu da bakina.

5Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na;ka kiyaye rabona,

6Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi;tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa.

7Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara;ko da dare ma zuciyata kan koya mini.

8Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

9Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;jikina kuma zai zauna lafiya,

10domin ba za ka yashe ni a kabari ba,ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

11Ka sanar da ni hanyar rai;za ka cika ni da farin ciki a gabanka,da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]