Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 142 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Maskil ne ta Dawuda. Sa’ad da yake cikin kogo. Addu’a ce.

1Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji;na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai.

2Na kawo gunagunina a gabansa;a gabansa na faɗa wahalata.

3Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina,kai ne wanda ya san hanyata.A hanyar da nake tafiyamutane sun kafa mini tarko.

4Duba ta damata ka gani;babu wanda ya kula da ni.Ba ni da mafaka;babu wanda ya kula da raina.

5Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;Na ce, “Kai ne mafakata,rabona a ƙasar masu rai.”

6Ka saurari kukata,gama ina cikin matsananciyar bukata;ka cece ni daga waɗanda suke fafarata,gama sun fi ni ƙarfi sosai.

7Ka ’yantar da ni daga kurkuku,don in yabi sunanka.Ta haka masu adalci za su taru kewaye da nisaboda alherinka gare ni.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]