Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 1 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

LITTAFI NA ƊAYA

1Mai farin ciki ne mutuminda ba ya aiki da shawarar mugayeko yă yi abin da masu zunubi suke yiko yă zauna tare da masu yin ba’a.

2Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,kuma yana ta nazarinta dare da rana.

3Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,wanda yake ba da amfani a daidai lokaciwanda kuma ganyensa ba sa bushewa.Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

4Ba haka yake da mugaye ba!Su kamar yayi neda iska take kwashewa.

5Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba,balle a sami masu zunubi a taron adalai.

6Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa,amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]