Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 20 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

1Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala;bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.

2Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarkiyă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.

3Bari yă tuna da dukan sadakokinkayă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. Sela

4Bari yă biya maka bukatan rankayă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.

5Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasaramu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu.Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka.

6Yanzu na san cewa,Ubangiji yakan cece shafaffensa.Yakan amsa masa daga samansa mai tsarkida ikon ceto na hannun damansa.

7Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai,amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.

8Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi,amma mu za mu tashi mu tsaya daram.

9Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki!Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira!

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]