Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 19 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

1Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;sararin sama suna furta aikin hannuwansa.

2Kowace rana tana yin jawabi;kowane dare yana nuna sani.

3Ba magana, ba kalmar da aka hurta,ba wani amon da aka ji daga gare su.

4Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya,kalmominsu zuwa iyakokin duniya.A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,

5wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa,kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.

6Takan taso daga ƙarshen sammaita kewaye zuwa wancan;babu abin da yake ɓuya wa zafinta.

7Dokar Ubangiji cikakkiya ce,takan wartsakar da rai.Farillan Ubangiji abin dogara ne,suna mai da hikima da sauƙi.

8Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne,suna ba da farin ciki ga zuciya.Umarnan Ubangiji haske nesuna ba da haske ga idanu.

9Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya,zai kasance har abada.Farillan Ubangiji tabbatattu ne,kuma gaba ɗaya masu adalci ne.

10Sun fi zinariya daraja,fiye da zalla zinariya nesa;sun fi zuma zaƙifiye da zuma daga kaki.

11Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka;a kiyaye su akwai lada mai girma.

12Wane ne zai iya rabe kurakuransa?Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa.

13Ka kiyaye bawanka daga zunubin ganganci;kada ka bari su yi mulki a kaina.Ta haka zan zama marar laifi;marar laifi na babban tawaye.

14Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyatasu zama abin gamsuwa a gabanka,Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]