Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 21 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

1Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka.Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!

2Ka biya masa bukatar zuciyarsaba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela

3Ka marabce shi da yalwar albarkaka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa.

4Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi,tsawo kwanaki, har abada abadin

5Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce;ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.

6Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarkaka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.

7Gama sarki ya dogara gare ka Ubangijita wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukakaba zai jijjigu ba.

8Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka;hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka.

9A lokacin bayyanarkaza ka sa su zama kamar wutar matoya.Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su,kuma wutarsa za tă cinye su.

10Za ka hallaka ’ya’yansu daga duniya,zuriyarsu kuma daga ’yan adam.

11Ko da yake suna shirya maka muguntasuna kuma ƙirƙiro mugayen dabaru, ba za su yi nasara ba;

12gama za ka sa su juye bayansusa’ad da ka auna su da bakan da ka ja.

13Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka;za mu rera mu kuma yabi ikonka.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]