Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 137 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

1A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kukasa’ad da muka tuna da Sihiyona.

2A can a kan rassan itatuwamuka rataye garayunmu,

3gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi,masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki;suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”

4Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangijia baƙuwar ƙasa?

5In na manta da ke, ya Urushalima,bari hannuna na dama manta da iyawarsa.

6Bari harshena yă manne wa rufin bakinain ban tuna da ke ba,in ban so Urushalimafarin cikin mafi girma ba.

7Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yia ranar da Urushalima ta fāɗi.Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta,A ragargaza ta har tushenta!”

8Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka,mai farin ciki ne wanda ya sāka mikisaboda abin da kika yi mana,

9shi da ya ƙwace jarirankiya fyaɗa su a kan duwatsu.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]