Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Psalms 138 OHCB

Side by side with the Father's Heart Bible™

Ta Dawuda.

1Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;a gaban “alloli” zan rera yabo.

2Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarkizan kuma yabi sunankasaboda ƙaunarka da amincinka,saboda ka ɗaukaka a bisa komesunanka da kuma maganarka.

3Sa’ad da na kira, ka amsa mini;ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni.

4Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji,sa’ad da suka ji maganganun bakinka.

5Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji,gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.

6Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu,amma tun da nesa ya san masu girman kai.

7Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala,kana kiyaye raina;ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana,da hannunka na dama ka cece ni.

8Ubangiji zai cika manufarsa a kaina;ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada,kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]