Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 18 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Whoever isolates himself pursues his own desire; he lashes out against all sound wisdom. Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai; yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai.
2 A fool takes no pleasure in understanding, but only in airing his own opinions. Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.
3 When wickedness comes, contempt comes too, and with dishonor comes reproach. Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo, haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo.
4 The words of a person's mouth are deep waters; the fountain of wisdom is a flowing stream. Kalmomin bakin mutum suna da zurfi kamar ruwaye, amma maɓulɓulan hikima rafi ne mai gudu.
5 It is not good to show partiality to the wicked, denying justice to the righteous. Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri ko ka hana wa marar laifi adalci.
6 A fool's lips bring strife, and his mouth invites a beating. Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa, bakinsa kuma kan gayyaci dūka.
7 A fool's mouth is his ruin, and his lips are a snare to his soul. Bakin wawa lalatar da kansa yake yi leɓunansa kuma tarko ne ga ransa.
8 The words of a gossip are like choice morsels; they go down into the inmost being. Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke; sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.
9 Whoever is slack in his work is brother to one who destroys. Wanda yake ragwanci a aikinsa ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.
10 The name of our Father is a strong tower; the righteous runs into it and is safe. Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi; masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
11 A rich man's wealth is his fortified city; in his imagination it is like a high wall. Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga; suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba.
12 Before destruction the human heart is proud, but humility comes before honor. Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai, amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
13 If one answers before he listens, it is his foolishness and his shame. Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara, wannan wauta ce da kuma abin kunya.
14 A person's spirit can sustain him through sickness, but a crushed spirit—who can bear it? Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo, amma in ya karai, to, tasa ta ƙare.
15 The discerning heart acquires knowledge, and the ear of the wise seeks it out. Zuciya mai la’akari kan nemi sani; kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya.
16 A person's gift opens the way for him and brings him before important people. Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa yakan kuma kai shi a gaban babban mutum.
17 The first to state his case seems right, until another comes and examines him. Wanda ya fara mai da jawabi yakan zama kamar shi ne mai gaskiya, sai wani ya fito ya yi masa tambaya tukuna.
18 Casting the lot settles disputes and separates strong opponents. Jefa ƙuri’a kan daidaita tsakanin masu faɗa ta kuma ajiye masu faɗan a rabe.
19 An offended brother is harder to win than a fortified city, and disputes are like the bars of a fortress. Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa, kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.
20 From the fruit of a person's mouth his stomach is satisfied; with the yield of his lips he is filled. Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika; girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi.
21 Death and life are in the power of the tongue, and those who love it will eat its fruit. Harshe yana da ikon rai da mutuwa, kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.
22 He who finds a wife finds what is good and receives favor from our Father. Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
23 The poor person pleads for mercy, but the rich answers harshly. Matalauci kan yi roƙo da taushi, amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya.
24 A man of many companions may come to ruin, but there is a friend who sticks closer than a brother. Mutum mai abokai masu yawa kan lalace, amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]