Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 17 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Better a dry crust eaten in peace than a house full of feasting with strife. Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.
2 A prudent servant will rule over a disgraceful son and will share the inheritance among the brothers. Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa.
3 The crucible is for silver and the furnace for gold, but our Father tests hearts. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.
4 An evildoer listens to wicked lips; a liar listens to a destructive tongue. Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna; maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.
5 Whoever mocks the poor insults his Maker; whoever gloats over disaster will not go unpunished. Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne; duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi.
6 Grandchildren are the crown of the aged, and the glory of children is their parents. Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.
7 Fine speech is not fitting for a fool—still less are lying lips for a noble. Leɓunan basira ba su dace da wawa ba, ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya!
8 A bribe seems like a magic charm to the one who gives it; wherever he turns, he thinks he will succeed. Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi; ko’ina ya juye, yakan yi nasara.
9 Whoever covers an offense seeks love, but whoever keeps bringing it up separates close friends. Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.
10 A rebuke goes deeper into a person of understanding than one hundred blows into a fool. Tsawata kan sa mutum ya koyi basira fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.
11 A rebellious man seeks only evil, and a cruel messenger will be sent against him. Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah; za a aika manzo mutuwa a kansu.
12 Better to meet a bear robbed of her cubs than a fool in his foolishness. Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa.
13 If anyone returns evil for good, evil will never leave his house. In mutum ya sāka alheri da mugunta, mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba.
14 Starting a quarrel is like breaching a dam, so drop the dispute before it bursts out. Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.
15 Whoever justifies the wicked and whoever condemns the righteous—both alike are detestable to our Father. Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu.
16 Why should a fool have money in hand to buy wisdom, when he has no heart to learn? Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa, da yake ba shi da sha’awar samun hikima?
17 A friend loves at all times, and a brother is born for a time of trouble. Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.
18 One who lacks sense shakes hands on a pledge and puts up security for his neighbor. Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci.
19 Whoever loves wrongdoing loves strife; whoever builds his gate high invites destruction. Duk mai son faɗa yana son zunubi, duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka.
20 A crooked heart finds no good, and a twisted tongue falls into trouble. Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba; duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala.
21 Whoever fathers a fool brings grief on himself; the father of a godless fool has no joy. Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki babu farin ciki ga mahaifin wawa.
22 A joyful heart is good medicine, but a crushed spirit dries up the bones. Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
23 A wicked man takes a bribe in secret to pervert the ways of justice. Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce don yă lalace yin adalci.
24 A discerning person keeps wisdom in view, but the eyes of a fool wander to the ends of the earth. Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima, amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya.
25 A foolish son is a grief to his father and bitterness to the mother who bore him. Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.
26 To punish the righteous is not good, nor to flog the noble for their integrity. Ba shi da kyau a hukunta marar laifi, ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu.
27 Whoever holds back his words has knowledge, and one with a calm spirit is a person of understanding. Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi, mutum mai basira kuma natsattse ne.
28 Even a fool who keeps silent is thought wise; when he closes his lips, he seems discerning. Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]