Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 16 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The plans of the heart belong to man, but the answer of the tongue comes from our Father. Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke, amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.
2 All a man's ways are pure in his own eyes, but our Father weighs the motives. Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi, amma Ubangiji yakan auna manufofi.
3 Commit your works to our Father, and your plans will be established. Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
4 Our Father has made everything for its purpose, even the wicked for the day of trouble. Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa, har ma da mugaye domin ranar masifa.
5 Everyone proud of heart is detestable to our Father; be assured, he will not go unpunished. Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.
6 Loving devotion and faithfulness atone for sin, and the fear of our Father turns a person away from evil. Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi; ta wurin tsoron Ubangiji mutum kan guji mugunta.
7 When a man's ways please our Father, our Father makes even the man's enemies live at peace with him. Sa’ad da hanyoyin mutum sun gamshi Ubangiji, yakan sa abokan gāban mutumin ma su zauna lafiya da shi.
8 Better a little with righteousness than great income with injustice. Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci da sami riba mai yawa ta hanyar rashin gaskiya.
9 The heart of man plans his way, but our Father establishes his steps. ’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu, amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.
10 A divine verdict is on the lips of a king; his mouth does not betray justice. Leɓunan sarki kan yi magana kamar ta wurin ikon Allah, kuma bai kamata bakinsa ya yi kuskure a yanke shari’a ba.
11 Honest scales and balances belong to our Father; every weight and measure is his work. Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne; dukan ma’aunai da suke cikin jaka yinsa ne.
12 It is detestable for kings to do wickedness, for a throne is established through righteousness. Sarakuna suna ƙyamar abin da ba shi da kyau, gama an kafa kujerar sarauta ta wurin adalci ne.
13 Righteous lips are the delight of kings, and they love the one who speaks what is right. Sarakuna sukan ji daɗi leɓuna masu yin gaskiya; sukan darjanta mutumin da yake faɗin gaskiya.
14 A king's wrath is a messenger of death, but a wise man will appease it. Fushin sarki ɗan saƙon mutuwa ne, amma mai hikima yakan faranta masa rai.
15 In the light of a king's face is life, and his favor is like a cloud bringing the spring rain. Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan; tagomashinsa yana kamar girgijen ruwa a bazara.
16 How much better to get wisdom than gold! Getting understanding is worth more than silver. Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya, ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!
17 The highway of the upright turns away from evil; whoever guards his way protects his life. Buɗaɗɗiyar hanyar masu aikata gaskiya kan guje wa mugunta; duk wanda yake lura da hanyarsa yakan lura da ransa.
18 Pride goes before destruction, and a haughty spirit before a fall. Girmankai yakan zo kafin hallaka, girman kai yakan zo kafin fāɗuwa.
19 Better to be lowly in spirit among the poor than to share the plunder with the proud. Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu sauƙinkai, da ka raba ganima da masu girman kai.
20 Whoever heeds the word will find good, and blessed is the one who trusts in our Father. Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara, kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji.
21 The wise of heart is called discerning, and pleasant speech increases persuasiveness. Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai, kuma kalmomi masu daɗi kan inganta umarni.
22 Understanding is a fountain of life to the one who has it, but fools are corrected by their own foolishness. Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi, amma wauta kan kawo hukunci ga wawaye.
23 The heart of the wise makes his speech wise and adds persuasiveness to his lips. Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa, kuma leɓunansa kan inganta umarni.
24 Pleasant words are a honeycomb, sweet to the soul and healing to the bones. Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma, mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.
25 There is a way that seems right to a man, but its end is the way of death. Akwai hanyar da ta yi kamar daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.
26 A worker's appetite works for him; his hunger drives him on. Marmarin cin abinci yakan yi wa ɗan ƙodago aiki; yunwarsa kan sa ya ci gaba.
27 A worthless man digs up evil, and on his lips is a scorching fire. Mutumin banza yakan ƙulla mugunta, kuma jawabinsa yana kama da wuta mai ƙuna.
28 A perverse man spreads strife, and a gossip separates close friends. Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.
29 A violent man entices his neighbor and leads him down a harmful path. Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa ya kai shi a hanyar da ba ta da kyau.
30 Whoever winks his eyes plots perversity; whoever purses his lips is bent on evil. Duk wanda ya ƙyifce da idonsa yana ƙulla maƙarƙashiya ce; duk wanda ya murguɗa leɓunansa yana niyya aikata mugunta ke nan.
31 Gray hair is a crown of glory; it is gained in the way of righteousness. Furfura rawani ne mai daraja; akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.
32 Better a patient person than a mighty one, and one who rules his spirit than one who takes a city. Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi, ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.
33 The lot is cast into the lap, but its every decision is from our Father. Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]