Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 15 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 A gentle answer turns away wrath, but a harsh word stirs up anger. Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.
2 The tongue of the wise commends knowledge, but the mouths of fools pour out foolishness. Harshen mai hikima kan yi zance mai kyau a kan sani, amma bakin wawa kan fitar da wauta.
3 The eyes of our Father are in every place, keeping watch on the evil and the good. Idanun Ubangiji suna a ko’ina, suna lura da masu aikata mugunta da masu aikata alheri.
4 A gentle tongue is a tree of life, but a corrupt tongue crushes the spirit. Harshen da ya kawo warkarwa shi ne itacen rai, amma harshe mai ƙarya kan ragargaza zuciya.
5 A fool despises his father's instruction, but whoever heeds correction is prudent. Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa, amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.
6 In the house of the righteous there is much treasure, but the income of the wicked brings trouble. Gidan adali yana da dukiya mai yawa, amma albashin mugaye kan kawo musu wahala.
7 The lips of the wise spread knowledge, but not so the hearts of fools. Leɓunan masu hikima sukan baza sani; ba haka zukatan wawaye suke ba.
8 The sacrifice of the wicked is detestable to our Father, but the prayer of the upright is his delight. Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye, amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi.
9 The way of the wicked is detestable to our Father, but he loves the one who pursues righteousness. Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci.
10 There is severe discipline for the one who leaves the path, and whoever hates correction will die. Horo mai tsanani yana jiran duk wanda ya bar hanya; wanda ya ƙi gyara zai mutu.
11 The grave and Destruction lie open before our Father; how much more the hearts of all people! Mutuwa da Hallaka suna nan a fili a gaban Ubangiji, balle fa zukatan mutane!
12 A scoffer does not love to be corrected; he will not go to the wise. Mai yin ba’a yakan ƙi gyara; ba zai nemi shawara mai hikima ba.
13 A glad heart makes a cheerful face, but a sorrowful heart crushes the spirit. Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske, amma ciwon zuciya kan ragargaza rai.
14 A discerning heart seeks knowledge, but the mouths of fools feed on foolishness. Zuciya mai la’akari kan nemi sani, amma bakin wawa wauta ce ke ciyar da shi.
15 All the days of the afflicted are hard, but a cheerful heart has a continual feast. Dukan kwanakin mutumin da ake danniya fama yake yi, amma zuciya mai farin ciki yana yin biki kullum.
16 Better a little with the fear of our Father than great treasure and trouble with it. Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.
17 Better a meal of vegetables where there is love than a fattened ox with hatred. Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take.
18 A hot-tempered man stirs up strife, but one who is slow to anger calms a quarrel. Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa.
19 The way of the lazy is like a hedge of thorns, but the path of the upright is a level highway. An tare hanyar rago da ƙayayyuwa, amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce.
20 A wise son makes a glad father, but a foolish man despises his mother. Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa, amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.
21 Foolishness is joy to one who lacks sense, but a person of understanding walks a straight path. Wauta kan sa mutum marar azanci ya yi farin ciki, amma mai basira kan kiyaye abin da yake yi daidai.
22 Plans fail without counsel, but with many advisers they succeed. Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara.
23 A person finds joy in giving an apt reply, and how good is a word at the right time! Mutum yakan yi farin ciki a ba da amsar da take daidai, kuma ina misali a yi magana a lokacin da ya dace!
24 The path of life leads upward for the prudent, turning him away from the grave below. Hanyar rai na yin jagora ya haura wa masu hikima don ta kiyaye shi daga gangarawa zuwa kabari.
25 Our Father tears down the house of the proud, but he protects the widow's boundary. Ubangiji yakan rushe gidan mai girman kai amma yakan kiyaye iyakokin gwauruwa daidai.
26 The thoughts of the wicked are detestable to our Father, but gracious words are pure. Ubangiji yana ƙyamar tunanin mugaye, amma waɗanda suke da tunani masu tsabta yakan ji daɗinsu.
27 Whoever is greedy for unjust gain brings trouble on his own household, but the one who hates bribes will live. Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa, amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu.
28 The heart of the righteous weighs how to answer, but the mouth of the wicked pours out evil. Zuciyar mai adalci takan auna amsoshinta, amma bakin mugu yakan fitar da mugunta.
29 Our Father is far from the wicked, but he hears the prayer of the righteous. Ubangiji yana nesa da mugaye amma yakan ji addu’ar adalai.
30 The light of the eyes brings joy to the heart, and good news refreshes the bones. Fuska mai fara’a takan kawo farin ciki ga zuciya, kuma labari mai daɗi na kawo lafiya ga ƙasusuwa.
31 The ear that listens to life-giving correction will dwell among the wise. Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba.
32 Whoever ignores instruction despises himself, but whoever listens to correction gains understanding. Duk waɗanda suka ƙi horon sun rena kansu ke nan, amma duk waɗanda sun yarda da gyara sukan ƙara basira.
33 The fear of our Father is the instruction of wisdom, and humility comes before honor. Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima, kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]