Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 14 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The wisest of women builds her house, but foolishness tears hers down with her own hands. Mace mai hikima kan gina gidanta, amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.
2 Whoever walks in uprightness fears our Father, but one whose ways are crooked despises him. Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji, amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi.
3 A fool's mouth is a rod for his own pride, but the lips of the wise protect them. Maganar wawa kan kawo sanda a bayansa, amma leɓunan masu hikima kan tsare su.
4 Where there are no oxen, the manger stays clean, but an abundant harvest comes through the strength of an ox. Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome, amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito.
5 A faithful witness does not lie, but a false witness breathes out lies. Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu, amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi.
6 The scoffer seeks wisdom and finds none, but knowledge comes easily to the discerning. Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome, amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira.
7 Stay away from a fool, for you will find no knowledge on his lips. Ka guji wawa, gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.
8 The wisdom of the prudent is to discern their way, but the foolishness of fools is deceit. Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu, amma wautar wawaye ruɗu ne.
9 Fools mock the guilt offering, but among the upright there is favor. Wawaye kan yi ba’a a gyaran zunubi, amma fatan alheri yana samuwa a cikin masu aikata gaskiya.
10 The heart knows its own bitterness, and no stranger shares in its joy. Kowace zuciya ta san ɓacin ranta, kuma babu wani dabam da zai yi rabon jin daɗinsa.
11 The house of the wicked will be destroyed, but the tent of the upright will flourish. Za a rushe gidan mugu, amma tentin mai aikata gaskiya zai haɓaka.
12 There is a way that seems right to a person, but its end is the way of death. Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.
13 Even in laughter the heart may ache, and the end of joy may be grief. Ko cikin dariya zuciya takan yi ciwo, kuma farin ciki kan iya ƙarasa a baƙin ciki.
14 The backslider in heart will be filled with the fruit of his ways, and a good person with the fruit of his. Marasa bangaskiya za su sami sakamako cikakke saboda hanyoyinsu, kuma mutumin kirki zai sami lada saboda nasa.
15 The simple believe anything, but the prudent give thought to their steps. Marar azanci kan gaskata kome, amma mai la’akari kan yi tunani game da matakinsa.
16 The wise fear and turn away from evil, but a fool is reckless and overconfident. Mai hikima kan ji tsoron Ubangiji ya kuma guji mugunta, amma wawa yana da girman kai yakan yi kome da garaje.
17 A quick-tempered person acts foolishly, and one who plots evil schemes is hated. Mutum mai saurin fushi yakan yi ayyukan wauta, akan kuma ƙi mai son nuna wayo.
18 The simple inherit foolishness, but the prudent are crowned with knowledge. Marar azanci kan gāji wauta, amma mai la’akari kan sami rawanin sani.
19 The evil bow down before the good, and the wicked at the gates of the righteous. Masu mugunta za su rusuna a gaban masu kirki, mugaye kuma za su yi haka a ƙofofin adalai.
20 The poor are shunned even by their neighbors, but the rich have many friends. Maƙwabta sukan gudu daga matalauta, amma masu arziki suna da abokai da yawa.
21 Whoever despises his neighbor sins, but blessed is the one who is kind to the poor. Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata.
22 Do not those who plot evil go astray? But covenant love and faithfulness belong to those who plan good. Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci.
23 In all hard work there is profit, but mere talk leads only to poverty. Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.
24 The crown of the wise is their wealth, but the foolishness of fools yields only foolishness. Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu, amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai.
25 A truthful witness saves lives, but one who breathes out lies is treacherous. Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka, amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne.
26 In the fear of our Father is strong confidence, and his children will have a refuge. Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka, kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.
27 The fear of our Father is a fountain of life, turning a person away from the snares of death. Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.
28 A large population is a king's glory, but without people a prince is ruined. Yawan mutane shi ne ɗaukakar sarki, amma in ba tare da mabiya ba sarki ba kome ba ne.
29 Whoever is slow to anger has great understanding, but a hot temper exalts foolishness. Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa, amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.
30 A tranquil heart gives life to the body, but envy rots the bones. Zuciya mai salama kan ba jiki rai, amma kishi kan sa ƙasusuwa su yi ciwo.
31 Whoever oppresses the poor reproaches our Father, their Maker, but whoever is kind to the needy honors him. Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.
32 The wicked are brought down by their own evil, but the righteous find refuge even in death. Sa’ad bala’i ya auku, mugaye kan fāɗi, amma ko a mutuwa masu adalci suna da mafaka.
33 Wisdom rests in the heart of the discerning, but even among fools it makes itself known. Hikima tana a zuciyar mai azanci, kuma ko a cikin wawaye takan sa a santa.
34 Righteousness exalts a nation, but sin is a disgrace to any people. Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane.
35 A king's favor rests on a wise servant, but his wrath falls on one who acts shamefully. Sarki yakan yi murna a kan bawa mai hikima, amma bawa marar kunya kan jawo fushinsa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]