Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 13 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 A wise son heeds his father's instruction, but a scoffer does not listen to rebuke. Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa, amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.
2 From the fruit of his mouth a person enjoys good things, but the appetite of the treacherous is for violence. Daga abin da ya fito leɓunan mutum ne mutum kan ji daɗin abubuwa masu kyau, amma marar aminci yakan ƙosa ya tā-da-na-zaune-tsaye.
3 Whoever guards his mouth protects his life, but one who opens his lips wide comes to ruin. Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa, amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci.
4 The lazy person craves and gets nothing, but the appetite of the diligent is richly satisfied. Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.
5 The righteous hates falsehood, but the wicked brings shame and disgrace. Adali yana ƙin abin da yake ƙarya, amma mugu kan jawo kunya da ƙasƙanci.
6 Righteousness guards the one whose way is blameless, but wickedness overthrows the sinner. Adalci yakan lura da mutum mai mutunci, amma mugunta takan sha kan mai zunubi.
7 One person pretends to be rich, yet has nothing; another pretends to be poor, yet has great wealth. Wani mutum yakan ɗauki kansa mai arziki ne, alhali ba shi da kome, wani ya ɗauki kansa shi matalauci ne, alhali shi mawadaci ne ƙwarai.
8 A person's wealth may ransom his life, but the poor hears no threat. Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa, amma matalauci ba ya jin barazana.
9 The light of the righteous shines joyfully, but the lamp of the wicked will be snuffed out. Hasken masu adalci kan haskaka ƙwarai, amma fitilar mugaye mutuwa take.
10 Arrogance breeds nothing but strife, but wisdom is with those who seek advice. Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.
11 Wealth gained by fraud dwindles away, but whoever gathers little by little makes it grow. Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
12 Hope deferred makes the heart sick, but desire fulfilled is a tree of life. Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo, amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
13 Whoever despises the word brings ruin on himself, but the one who reveres the commandment will be rewarded. Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa, amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada.
14 The teaching of the wise is a fountain of life, turning a person away from the snares of death. Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne, mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.
15 Good sense wins favor, but the way of the treacherous is their undoing. Fahimta mai kyau kan sami tagomashi, amma hanyar marar aminci tana da wuya.
16 Every prudent person acts with knowledge, but a fool flaunts his foolishness. Kowane mai azanci yakan nuna sani, amma wawa yakan yi tallen wawancinsa.
17 A wicked messenger falls into trouble, but a faithful envoy brings healing. Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala, amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa.
18 Poverty and shame come to whoever ignores discipline, but the one who heeds correction is honored. Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya, amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.
19 A desire fulfilled is sweet to the soul, but turning away from evil is detestable to fools. Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai, amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta.
20 Whoever walks with the wise grows wise, but the companion of fools suffers harm. Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima, amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
21 Disaster pursues sinners, but good rewards the righteous. Rashin sa’a kan fafare mai zunubi, amma wadata ce ladar adali.
22 A good person leaves an inheritance to his grandchildren, but the sinner's wealth is stored up for the righteous. Mutumin kirki kan bar gādo wa ’ya’ya ’ya’yansa, amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci.
23 The unplowed field of the poor could yield abundant food, but it is swept away for lack of justice. Gonar matalauci za tă iya ba da abinci a yalwace, amma rashin adalci kan share shi tas.
24 Whoever withholds the rod hates his son, but the one who loves him is diligent to discipline him. Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba, amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.
25 The righteous eats to his heart's content, but the belly of the wicked goes hungry. Masu adalci sukan ci isashen abinci, amma cikin mugaye na fama da yunwa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]