Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 12 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Whoever loves discipline loves knowledge, but whoever hates correction is senseless. Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani, amma duk mai ƙin gyara wawa ne.
2 A good man obtains favor from our Father, but he condemns the man who schemes evil. Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji, amma Ubangiji yakan hukunta mai son yin wayo.
3 No one is established by wickedness, but the root of the righteous will never be moved. Ba yadda mutum zai kahu ta wurin aikata mugunta, amma ba za a tumɓuke adali ba.
4 A wife of noble character is her husband's crown, but one who brings shame is like decay in his bones. Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne, amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa.
5 The plans of the righteous are just, but the advice of the wicked is deceitful. Shirye-shiryen masu adalci daidai ne, amma shawarar mugaye ruɗu ne.
6 The words of the wicked lie in wait for blood, but the speech of the upright rescues the innocent. Kalmomin mugu sukan kwanta suna jira su yi kisankai, amma jawabin masu aikata gaskiya kan kuɓutar da su.
7 The wicked are overthrown and are no more, but the house of the righteous will stand. Akan tumɓuke mugaye ba a ƙara ganinsu, amma gidan masu adalci kan tsaya daram.
8 A person is praised according to their good sense, but one with a warped mind is despised. Akan yabi mutum bisa ga hikimarsa, amma mutane marasa azanci akan rena su.
9 Better to be lowly and have a servant than to pretend to greatness and go hungry. Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa da ka mai da kanka kai wani ne alhali kuwa ba ka da abinci.
10 The righteous care for the needs of their animals, but even the mercy of the wicked is cruel. Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa, amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta.
11 Whoever works their land will have plenty of food, but whoever chases worthless pursuits lacks sense. Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.
12 The wicked crave the plunder of evil men, but the root of the righteous yields fruit. Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane, amma saiwar masu adalci kan haɓaka.
13 An evil man is trapped by his sinful talk, but the righteous escapes from trouble. Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi, amma adali kan kuɓuta daga wahala.
14 From the fruit of their words a person is filled with good things, and the work of their hands comes back to reward them. Daga abubuwan da suke fitowa daga leɓunansa mutum kan cika da abubuwa masu kyau tabbatacce yadda aikin hannuwansa suke ba shi lada.
15 The way of a fool seems right in his own eyes, but the wise listen to advice. Hanyar wawa daidai take a gare shi, amma mai hikima kan saurari shawara.
16 A fool shows his anger at once, but the prudent overlook an insult. Wawa kan nuna fushinsa nan take, amma mai la’akari kan ƙyale zargi.
17 Whoever speaks the truth gives honest testimony, but a false witness tells lies. Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya, amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.
18 Reckless words pierce like a sword, but the tongue of the wise brings healing. Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.
19 Truthful lips endure forever, but a lying tongue lasts only a moment. Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada, amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.
20 Deceit fills the hearts of those who plot evil, but joy belongs to those who promote peace. Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.
21 No harm overtakes the righteous, but the wicked are full of trouble. Ba wani lahanin da zai sami masu adalci, amma mugaye suna da nasu cike da wahala.
22 Lying lips are detestable to our Father, but those who act faithfully are his delight. Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
23 The prudent keep their knowledge to themselves, but the heart of fools blurts out foolishness. Mai la’akari kan kiyaye saninsa wa kansa, amma zuciyar wawa kan yi ta tallar wawanci.
24 Diligent hands will rule, but laziness ends in forced labor. Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.
25 Anxiety weighs down the heart, but a kind word cheers it up. Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum, amma maganar alheri kan faranta masa rai.
26 The righteous guide their neighbor, but the way of the wicked leads them astray. Adali yakan yi hankali a abokantaka, amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.
27 The lazy do not roast their game, but the diligent prize their possessions. Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta, amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci.
28 In the path of righteousness there is life, and along that way there is no death. A hanyar adalci akwai rai; a wannan hanya akwai rashin mutuwa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]