Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 11 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Dishonest scales are an abomination to our Father, but accurate weights are his delight. Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba, amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.
2 When pride comes, then comes disgrace, but wisdom comes with the humble. Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo, amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.
3 The integrity of the upright guides them, but the crookedness of the treacherous destroys them. Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su, amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.
4 Wealth does not profit in the day of wrath, but righteousness delivers from death. Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi, amma adalci kan yi ceto daga mutuwa.
5 The righteousness of the blameless makes their way straight, but the wicked falls by his own wickedness. Adalcin marasa laifi kan miƙe hanyarsu, amma akan ƙasƙantar da mugaye ta wurin muguntarsu.
6 The righteousness of the upright delivers them, but the treacherous are trapped by their own craving. Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su, amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace.
7 When a wicked person dies, his hope perishes, and his confidence in his own strength comes to nothing. Sa’ad da mugu ya mutu, sa zuciyarsa kan hallaka; dukan abin da ya sa zuciya daga ikonsa ba ya amfana kome.
8 The righteous is delivered from trouble, and the wicked comes into it in his place. Akan kuɓutar da mai adalci daga wahala, sai ta dawo wa mugu a maimako.
9 With his mouth the godless destroys his neighbor, but through knowledge the righteous are delivered. Da bakinsa marar sanin Allah kan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin sani mai adalci kan kuɓuta.
10 When things go well for the righteous, the city rejoices, and when the wicked perish, there are shouts of joy. Sa’ad da adali ya yi nasara, birnin kan yi farin ciki; sa’ad da mugu ya hallaka, akwai sowa ta farin ciki.
11 By the blessing of the upright a city is exalted, but by the mouth of the wicked it is torn down. Ta wurin albarkar mai aikata gaskiya birni kan ƙasaita, amma ta wurin bakin mugu akan hallaka birnin.
12 Whoever despises his neighbor lacks sense, but a person of understanding stays silent. Mutum da ba shi da azanci kan ki maƙwabci, amma mutum mai fahimi kan ƙame harshensa.
13 A gossip goes about revealing secrets, but someone with a trustworthy spirit can keep a secret. Gulma yakan lalace yarda, amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri.
14 Where there is no guidance, a people falls, but in an abundance of counselors there is safety. Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi, amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara.
15 Whoever puts up security for a stranger will surely suffer for it, but whoever hates shaking hands on a pledge is secure. Duk wanda ya ɗauki lamunin wani tabbatacce zai sha wahala, amma duk wanda ya ƙi ya sa hannu a ɗaukar lamuni ba ruwansa.
16 A gracious woman attains honor, and ruthless men attain riches. Mace mai hankali na samu bangirma, amma azzalumai za su sami dukiya.
17 A kind person benefits himself, but a cruel person brings trouble on himself. Mutumin kirki kan ribance kansa, amma mugu kan kawo wa kansa wahala.
18 The wicked earns deceptive wages, but whoever sows righteousness earns a true reward. Mugun mutum kan sami albashin ƙarya amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce.
19 Whoever is steadfast in righteousness finds life, but whoever pursues evil runs to his own death. Mutum mai adalci da gaske yakan sami rai, amma shi da ya duƙufa ga aikata mugunta kan tarar da mutuwarsa.
20 Those of crooked heart are an abomination to our Father, but those whose ways are blameless are his delight. Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi.
21 You can be sure the evil person will not go unpunished, but the children of the righteous will go free. Ka tabbata da wannan. Mugaye ba za su tafi babu hukunci ba, amma waɗanda suke masu adalci za su tafi babu hukunci.
22 Like a gold ring in a pig's snout is a beautiful woman who shows no discretion. Kamar zinariya a hancin alade haka kyan mace wadda ba ta da hankali.
23 The desire of the righteous ends only in good, but the hope of the wicked ends in wrath. Sha’awar adalai kan ƙare kawai a aikata alheri, amma sa zuciyar mugaye kan ƙarasa kawai a fushi.
24 One person gives freely, yet grows all the richer; another withholds what is right, only to end up in need. Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye; wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci.
25 A generous soul will be enriched, and whoever refreshes others will himself be refreshed. Mutum mai kyauta zai azurta; shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.
26 The people curse whoever holds back grain, but the one who sells it is blessed. Mutane kan la’anci mai ɓoye hatsi yana jira ya yi tsada, amma albarka kan zauna a kan wanda yake niyya ya sayar.
27 Whoever diligently seeks good seeks favor, but whoever searches for evil, evil will come to him. Duk mai nema alheri kan sami alheri, amma mugu kan zo wa wanda yake nemansa.
28 Whoever trusts in his riches will fall, but the righteous will flourish like green leaves. Duk wanda ya dogara ga arzikinsa zai fāɗi, amma adali zai yi nasara kamar koren ganye.
29 Whoever brings trouble on his own household will inherit the wind, and the fool will be servant to the wise of heart. Duk wanda ya kawo wahala wa iyalinsa zai gāji iska kawai, kuma wawa zai zama bawan masu hikima.
30 The fruit of the righteous is a tree of life, and whoever wins souls is wise. ’Ya’yan itacen adali itacen rai ne, kuma duk mai samun rayuka mai hikima ne.
31 If the righteous is repaid on earth, how much more the wicked and the sinner! In masu adalci sun sami abin da ya dace da su a duniya, yaya zai zama ga marasa sanin Allah da kuma masu zunubi!
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]