Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 10 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The proverbs of Solomon: A wise son brings joy to his father, but a foolish son brings grief to his mother. Karin maganar Solomon. Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
2 Treasures gained by wickedness do not profit, but righteousness rescues from death. Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.
3 Our Father will not let the righteous go hungry, but he thwarts the craving of the wicked. Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu.
4 Lazy hands make you poor, but diligent hands bring wealth. Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.
5 He who gathers in summer is a prudent son, but he who sleeps during harvest is a son who brings shame. Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.
6 Blessings rest on the head of the righteous, but the mouth of the wicked conceals violence. Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani, amma rikici kan sha bakin mugu.
7 The memory of the righteous is a blessing, but the name of the wicked will rot. Tunawa da mai adalci albarka ne amma sunan mugu zai ruɓe.
8 A wise heart accepts commands, but a babbling fool comes to ruin. Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni amma surutun wawa kan kai ga lalaci.
9 Whoever walks in integrity walks securely, but he who makes his ways crooked will be found out. Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.
10 Whoever winks causes trouble, and a babbling fool comes to ruin. Shi da ya ƙyifta ido da mugunta kan jawo baƙin ciki surutun wawa kuma kan zo da lalaci.
11 The mouth of the righteous is a fountain of life, but the mouth of the wicked conceals violence. Bakin adali maɓulɓulan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.
12 Hatred stirs up conflict, but love covers all offenses. Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.
13 On the lips of the discerning, wisdom is found, but a rod is for the back of one who lacks sense. Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi, amma bulala domin bayan marasa azanci ne.
14 The wise store up knowledge, but the mouth of a fool invites ruin. Mai hikima kan yi ajiyar sani, amma bakin wawa kan gayyaci lalaci.
15 The wealth of the rich is their fortified city; the ruin of the poor is their poverty. Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu, amma talauci shi ne lalacin matalauci.
16 The wage of the righteous leads to life; the gain of the wicked leads to sin. Hakkin adalai kan kawo musu rai, amma albashin mugaye kan kawo musu hukunci.
17 Whoever accepts discipline is on the path to life, but he who ignores correction leads others astray. Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai, amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.
18 Whoever conceals hatred is a liar, and whoever spreads slander is a fool. Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa, duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.
19 Where words are many, sin is never absent; but whoever holds his tongue is wise. Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki, amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.
20 The tongue of the righteous is choice silver; the heart of the wicked is worth little. Harshen adali azurfa ce zalla, amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani.
21 The lips of the righteous nourish many, but fools die for lack of sense. Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci.
22 The blessing of our Father brings wealth, and he adds no sorrow with it. Albarkar Ubangiji kan kawo wadata, ba ya kuma ƙara wahala a kai.
23 Doing wickedness is a game to a fool, but wisdom is the delight of a person of understanding. Wawa yakan ji daɗi halin mugunta, amma mutum mai fahimi kan ji daɗin hikima.
24 What the wicked dreads will come upon him, but the desire of the righteous will be granted. Abin da mugu ke tsoro shi ne zai same shi; abin da adali ke bukata yakan sami biyan bukata.
25 When the storm has passed, the wicked are gone, but the righteous are established forever. Sa’ad da hadiri ya taso, yakan watsar da mugaye, amma adalai za su tsaya daram har abada.
26 Like vinegar to the teeth and smoke to the eyes, so is the sluggard to those who send him. Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu, haka malalaci yake ga wanda ya aike shi.
27 The fear of our Father lengthens life, but the years of the wicked will be cut short. Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai, amma akan gajartar da shekarun mugaye.
28 The hope of the righteous brings joy, but the expectation of the wicked will perish. Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki, amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome.
29 The way of our Father is a refuge for the blameless, but ruin for those who do evil. Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta.
30 The righteous will never be shaken, but the wicked will not remain in the land. Ba za a taɓa tumɓuke masu adalci ba, amma mugaye ba za su ci gaba da kasance a ƙasar ba.
31 The mouth of the righteous yields wisdom, but the perverse tongue will be cut off. Bakin adalai kan fitar da hikima, amma za a dakatar da mugun harshe.
32 The lips of the righteous know what is acceptable, but the mouth of the wicked, only what is perverse. Leɓunan adalai sun san abin da ya dace, amma bakunan mugaye sun san abin da yake mugu ne kawai.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]