Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 9 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Wisdom has built her house; she has hewn out her seven pillars. Hikima ta gina gidanta; ta yi ginshiƙansa bakwai.
2 She has slaughtered her animals; she has mixed her wine; she has also set her table. Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta; ta kuma shirya teburinta.
3 She has sent out her young women to call from the highest places of the town: Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira daga wurare masu tsayi na birnin.
4 "Whoever is simple, let him come in here!" To the one who lacks sense she says, “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!” Tana faɗa wa marasa hankali.
5 "Come, eat my bread and drink the wine I have mixed. “Ku zo, ku ci abincina da ruwan inabin da na gauraye.
6 Leave your simple ways, and live; walk in the way of insight." Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu; yi tafiya a hanyar fahimi.
7 Whoever corrects a mocker brings abuse on himself, and whoever rebukes a wicked man gets hurt. “Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci.
8 Do not rebuke a mocker, or he will hate you; rebuke a wise man, and he will love you. Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka; ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.
9 Instruct a wise man and he will grow wiser; teach a righteous man and he will learn even more. Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima; ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa.
10 The fear of our Father is the beginning of wisdom, and the knowledge of the Holy One is insight. “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima, sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
11 For by me your days will be multiplied, and years will be added to your life. Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa, za a kuwa ƙara wa ranka shekaru.
12 If you are wise, you are wise for yourself; if you scoff, you alone will bear it. In kana da hikima, hikimarka za tă ba ka lada; in kai mai ba’a ne, kai kaɗai za ka sha wahala.”
13 The woman Folly is loud; she is naive and knows nothing. Wawancin mace a bayyane yake; ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani.
14 She sits at the door of her house, on a seat at the highest places of the town, Takan zauna a ƙofar gidanta, a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni,
15 calling to those who pass by, who are going straight on their way: tana kira ga masu wucewa, waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.
16 "Whoever is simple, let him come in here!" And to the one who lacks sense she says, “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!” Tana ce wa marasa hankali.
17 "Stolen water is sweet, and bread eaten in secret is pleasant." “Ruwan da aka sata ya fi daɗi; abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”
18 But he does not know that the dead are there, that her guests are in the depths of the grave. Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]