Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 8 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Does not Wisdom call out, and understanding raise her voice? Hikima ba ta yin kira ne? Fahimi ba ya tā da muryarsa ne?
2 Atop the heights along the way, where the paths meet, she takes her stand. A ƙwanƙoli a kan hanya, inda hanyoyi suka haɗu, ta ɗauki matsayinta;
3 Beside the gates, at the entrance to the city, at the doorways she cries aloud: kusa da ƙofofin shiga cikin birni, a mashigai, ta tā da murya,
4 "To you, all people, I call out; my voice reaches all humanity. “Gare ku, ya mutane, nake kira; na tā da muryata ga dukan ’yan adam.
5 You who are simple, learn prudence; you who are foolish, gain an understanding heart. Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali; ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi.
6 Listen, for I speak of noble things, and everything I say is right. Ku saurara, gama ina da abubuwa masu darajan da zan faɗa; na buɗe leɓunana don in faɗa abin da yake daidai.
7 My mouth utters truth, for my lips detest wickedness. Bakina yana magana abin da yake gaskiya, gama leɓunana sun ƙi mugunta.
8 All the words of my mouth are righteous; none of them is twisted or crooked. Dukan kalmomin bakina suna da adalci; babu waninsu da ya karkace ko kuwa ƙarya ne.
9 To the one who understands they are all clear, and right to those who find knowledge. Ga mai tunani dukansu daidai ne; ba su da laifi ga waɗanda suke da sani.
10 Take my instruction instead of silver, and knowledge rather than choice gold, Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa, sani a maimakon zinariya zalla,
11 for wisdom is better than jewels, and nothing you desire can compare with her. gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja, kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita.
12 I, Wisdom, dwell with prudence, and I find knowledge and discretion. “Ni, hikima, ina zama tare da hankali; ina da sani da iya rarrabewa.
13 The fear of our Father is to hate evil. Pride and arrogance, the evil way, and perverse speech I hate. Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta; ina ƙin girman kai da fariya, halin mugunta da kuma muguwar magana.
14 Counsel is mine, and sound wisdom; I am understanding; strength is mine. Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne; ina da fahimi da kuma iko.
15 By me kings reign, and rulers decree what is just; Ta wurina sarakuna suke mulki masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci;
16 by me princes govern, and nobles—all who rule with justice. ta wurina sarakuna suke mulki, da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.
17 I love those who love me, and those who search for me find me. Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, kuma waɗanda suke nemana sukan same ni.
18 With me are riches and honor, enduring wealth and righteousness. Tare da ni akwai wadata da girmamawa, dukiya da wadata masu dawwama.
19 My fruit is better than gold, than the finest gold, and what I yield surpasses choice silver. ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla; amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau.
20 I walk in the way of righteousness, along the paths of justice, Ina tafiya a hanyar adalci, a kan hanyoyin gaskiya,
21 giving wealth as an inheritance to those who love me, and filling their treasuries. ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata ina sa wuraren ajiyarsu su cika.
22 Our Father brought me forth at the beginning of his way, before his works of old. “Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa, kafin ayyukansa na tuntuni;
23 From ages past I was established, from the beginning, before the earth began. an naɗa ni tun fil azal, daga farko, kafin duniya ta kasance.
24 When there were no deep waters I was brought forth, when there were no springs overflowing with water. Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni, sa’ad da babu maɓulɓulai masu ruwa;
25 Before the mountains were settled, before the hills, I was brought forth, kafin a kafa duwatsu a wurarensu, kafin tuddai ma, an haife ni,
26 while he had not yet made the earth and its fields, or the first dust of the world. kafin ya yi duniya ko gonaki ko wata ƙurar duniya.
27 When he set the heavens in place, I was there; when he drew a circle over the face of the deep, Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa,
28 when he set the skies in place above, when he established the springs of the deep, sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram,
29 when he set for the sea its boundary so the waters would not cross their limits, when he marked out the foundations of the earth, sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa domin kada ruwaye su zarce umarninsa, da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya.
30 then I was beside him as a master craftsman, and I was his daily delight, rejoicing before him always, A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa. Na cika da murna kowace rana, kullum ina farin ciki a gabansa,
31 rejoicing in his whole world, and delighting in the human family. ina farin ciki da dukan duniyarsa ina murna da ’yan adam.
32 And now, my children, listen to me: blessed are those who keep my ways. “Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.
33 Listen to instruction and be wise; do not ignore it. Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima; kada ku ƙyale ta.
34 Blessed is the one who listens to me, watching daily at my gates, waiting beside my doorway. Mai albarka ne wanda ya saurare ni; yana tsaro kullum a ƙofofina, yana jira a ƙofar shigata.
35 For whoever finds me finds life and receives favor from our Father. Gama duk wanda ya same ni ya sami rai zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
36 But whoever misses me harms his own soul; all who hate me love death." Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa; dukan waɗanda suke ƙina suna ƙaunar mutuwa ke nan.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]