Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 7 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 My son, keep my words, and store up my commandments within you. Ɗana, ka kiyaye kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka.
2 Keep my commandments and live; guard my teaching as the apple of your eye. Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu; ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka.
3 Bind them on your fingers; write them on the tablet of your heart. Ka daure su a yatsotsinka; ka rubuta su a allon zuciyarka.
4 Say to wisdom, "You are my sister," and call understanding your dearest friend, Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,” ka kuma kira fahimi danginka;
5 to keep you from the forbidden woman, from the stranger with her smooth words. za su kiyaye ka daga mazinaciya, daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali.
6 For at the window of my house I looked down through my lattice, A tagar gidana na leƙa ta labule mai rammuka.
7 and I saw among the naive, I noticed among the young men, a youth who lacked sense, Sai na gani a cikin marasa azanci, na lura a cikin samari, wani matashi wanda ba shi da hankali.
8 passing through the street near her corner, taking the road to her house, Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta, yana tafiya a gefen wajen gidanta
9 in the twilight, as the day faded, in the dark of night and gloom. da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa, yayinda duhun dare yana farawa.
10 And there a woman comes to meet him, dressed like a prostitute, with cunning in her heart. Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi, saye da riga kamar karuwa shirye kuma don ta yaudare shi.
11 She is loud and defiant; her feet will not stay at home. (Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya, ƙafafunta ba sa zama a gida;
12 Now in the street, now in the squares, she lurks at every corner. wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali, tana yawo a kowace kusurwa.)
13 She grabs him and kisses him, and with a brazen face she says to him: Sai ta kama shi ta rungume shi da duban soyayya a fuskarta ta ce,
14 "I had peace offerings to bring; today I have paid my vows. “Ina da hadaya ta salama a gida; yau zan cika alkawarina.
15 So I came out to meet you, to look for you eagerly, and I have found you. Saboda haka na fito don in sadu da kai; na neme ka na kuma same ka!
16 I have spread my bed with coverings, with colored linens from Egypt. Na lulluɓe gadona da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.
17 I have perfumed my bed with myrrh, aloes, and cinnamon. Na yayyafa turare a gadona da mur, aloyes da kuma kirfa.
18 Come, let us drink deep of love until morning; let us lose ourselves in love. Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe; bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna!
19 For my husband is not at home; he has gone on a long journey. Mijina ba ya gida; ya yi tafiya mai nisa.
20 He took a bag of money with him and will not come home until the full moon." Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”
21 With all her persuasive words she sways him; with her smooth lips she draws him in. Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.
22 All at once he follows her, like an ox going to the slaughter, like a deer stepping into a snare, Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo
23 until an arrow pierces its liver; like a bird darting into a trap, he does not know it will cost him his life. sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.
24 Now then, my sons, listen to me, and pay attention to what I say. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.
25 Do not let your heart turn aside to her ways; do not wander into her paths. Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta.
26 For she has brought down many victims; her slain are a mighty multitude. Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.
27 Her house is the road to the grave, going down to the chambers of death. Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]