Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 6 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 My son, if you have put up security for your neighbor, if you have shaken hands in pledge for a stranger, Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi, in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani,
2 you have been snared by the words of your mouth, caught by the words of your mouth. in maganarka ta taɓa kama ka, ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,
3 Then do this, my son, and free yourself, for you are now at your neighbor's mercy: go, humble yourself, and plead with your neighbor. to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka; da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka, ka tafi ka ƙasƙantar da kanka; ka roƙi maƙwabcinka!
4 Give no sleep to your eyes, no slumber to your eyelids. Ka hana kanka barci, ko gyangyaɗi a idanunka ma.
5 Free yourself like a gazelle from the hand, like a bird from the hand of the trapper. Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.
6 Go to the ant, you sluggard; consider her ways and be wise. Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!
7 Without having any chief, officer, or ruler, Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki,
8 she prepares her bread in summer and gathers her food in harvest. duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
9 How long will you lie there, sluggard? When will you arise from your sleep? Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku?
10 A little sleep, a little slumber, a little folding of the hands to rest, Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,
11 and poverty will come upon you like a robber, and scarcity like an armed man. talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi.
12 A worthless person, a wicked man, goes about with crooked speech, Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki,
13 winks with his eyes, signals with his feet, points with his fingers, wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa,
14 with perverted heart he devises evil, continually sowing discord; wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye
15 therefore calamity will come upon him suddenly; in a moment he will be broken beyond healing. Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.
16 There are six things our Father hates, seven that are detestable to him: Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,
17 haughty eyes, a lying tongue, and hands that shed innocent blood, duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,
18 a heart that devises wicked plans, feet that hurry to run to evil, zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,
19 a false witness who breathes out lies, and one who sows discord among brothers. mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.
20 My son, keep your father's commandment, and do not forsake your mother's teaching. Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
21 Bind them on your heart always; tie them around your neck. Ka ɗaura su a zuciyarka har abada; ka ɗaura su kewaye da wuyanka.
22 When you walk, they will lead you; when you lie down, they will watch over you; and when you awake, they will talk with you. Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa’ad da kake barci, za su lura da kai; sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.
23 For the commandment is a lamp and the teaching a light, and the reproofs of discipline are the way of life, Gama waɗannan umarnai fitila ne, wannan koyarwa haske ne, kuma gyare-gyaren horo hanyar rayuwa ce,
24 to keep you from the evil woman, from the smooth tongue of the adulteress. suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a daga sulɓin harshen mace marar aminci.
25 Do not desire her beauty in your heart, and do not let her capture you with her eyelashes; Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.
26 for the price of a prostitute is only a loaf of bread, but a married woman hunts down a precious life. Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta, mazinaciya kuma takan farauci ranka.
27 Can a man carry fire next to his chest and his clothes not be burned? Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa ba tare da rigunansa sun ƙone ba?
28 Or can one walk on hot coals and his feet not be scorched? Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba?
29 So is he who sleeps with his neighbor's wife; none who touches her will go unpunished. Haka yake da wanda ya kwana da matar wani; babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci.
30 People do not despise a thief if he steals to satisfy his appetite when he is hungry, Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata don yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa.
31 but if he is caught, he will pay sevenfold; he will give all the goods of his house. Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai ko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa.
32 He who commits adultery lacks sense; he who does it destroys himself. Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali; duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.
33 He will get wounds and dishonor, and his disgrace will not be wiped away. Dūka da kunya ne za su zama rabonsa, kuma kunyarsa za tă dawwama.
34 For jealousy makes a man furious, and he will show no mercy in the day of vengeance. Gama kishi kan tā da hasalar miji, kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa.
35 He will accept no compensation; he will refuse no matter how large the bribe. Ba zai karɓi duk wata biya ba; zai ƙi cin hanci, kome yawansu.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]