Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 5 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 My son, pay attention to my wisdom; listen closely to my understanding, Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata ka saurara da kyau ga kalmomin basirata,
2 so that you may guard discretion and your lips may preserve knowledge. don ka ci gaba da yin kome daidai leɓunanka za su adana sani.
3 For the lips of the forbidden woman drip honey, and her mouth is smoother than oil, Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma, maganarta tana da sulɓi fiye da mai;
4 but in the end she is bitter as poison, sharp as a double-edged sword. amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya, mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.
5 Her feet go down to death; her steps take hold of the grave. Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa; sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari.
6 She gives no thought to the path of life; her ways wander, and she does not know it. Ba ta wani tunanin rayuwa; hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.
7 And now, my sons, listen to me, and do not turn away from the words of my mouth. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; kada ku juye daga abin da nake faɗa.
8 Keep your way far from her, and do not go near the door of her house, Ku yi nesa da hanyarta, kana ku je kusa da ƙofar gidanta,
9 lest you give your honor to others and your years to one who is cruel, don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu da kuma shekarunku ga wani marar imani,
10 lest strangers take their fill of your strength, and your hard-earned labors go to the house of a foreigner, don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.
11 and at your end you groan, when your flesh and body are consumed, A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi, sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.
12 and you say, "How I hated discipline, and my heart despised correction! Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo! Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!
13 I did not listen to the voice of my teachers or heed my instructors. Ban yi biyayya da malamaina ba ko in saurari masu koyar da ni.
14 I was at the brink of utter ruin in the midst of the assembled congregation." Na zo gab da hallaka gaba ɗaya a tsakiyar dukan taron.”
15 Drink water from your own cistern, flowing water from your own well. Ku sha ruwa daga tankinku, ruwa mai gudu daga rijiyarku.
16 Should your springs overflow in the streets, your streams of water in the public squares? In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje, rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?
17 Let them be yours alone, and not shared with strangers. Bari su zama naka kaɗai, don kada ka raba da baƙi.
18 May your fountain be blessed, and rejoice in the wife of your youth, Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka, bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.
19 a loving doe, a graceful deer. May her love satisfy you always; may you be captivated continually by her love. Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani, bari mamanta su ishe ka kullum, bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.
20 Why then, my son, should you be captivated by a forbidden woman and embrace another man's wife? Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali? Don me za ka rungume matar wani?
21 For a man's ways are before the eyes of our Father, and he examines all the man's paths. Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji, yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.
22 The wicked are caught by their own wrongdoing and held fast in the cords of their sin. Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi; igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan.
23 He will die for lack of discipline, and he will go astray because of his great foolishness. Zai mutu saboda rashin ɗa’a yawan wawancinsa zai sa yă kauce.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]