Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 4 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Listen, my children, to a father's instruction; pay attention, and gain understanding. Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi.
2 I am giving you sound teaching, so do not abandon my instruction. Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.
3 For I too was a son to my father, tender and the only beloved of my mother. Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,
4 He taught me and said, "Let your heart hold on to my words; keep my commands and you will live. ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.
5 Get wisdom, get understanding; do not forget, and do not turn away from the words of my mouth. Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.
6 Do not forsake her, and she will protect you; love her, and she will watch over you. Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.
7 The beginning of wisdom is this: get wisdom; and with all you acquire, get understanding. Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima. Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.
8 Cherish her, and she will lift you high; embrace her, and she will bring you honor. Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka; ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka.
9 She will set a garland of grace on your head; she will present you with a crown of glory." Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.”
10 Listen, my son, and receive my words, and the years of your life will be many. Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa, shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa.
11 I have taught you the way of wisdom; I have led you along straight paths. Na bishe ka a hanyar hikima na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi.
12 When you walk, your steps will not be held back; and when you run, you will not stumble. Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe; sa’ad da kake gudu, ba za ka fāɗi ba.
13 Hold on to instruction, do not let go; guard her, for she is your life. Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce; ka tsare shi sosai, gama ranka ne.
14 Do not set foot on the path of the wicked, and do not walk in the way of evildoers. Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye.
15 Avoid it, do not travel on it; turn away from it and pass on by. Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka.
16 For they cannot sleep unless they do wrong; they are robbed of rest unless they make someone stumble. Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta; ba su barci sai sun cuci wani.
17 They feed on the bread of wickedness and drink the wine of violence. Mugunta da ta’adi kamar ci da sha suke a gare su.
18 But the path of the righteous is like the light of dawn, shining brighter and brighter until the full light of day. Hanyar adali kamar fitowar rana ce, sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka.
19 The way of the wicked is like deep darkness; they do not know what makes them stumble. Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne; ba sa sanin abin da ya sa suke tuntuɓe.
20 My son, pay attention to my words; listen closely to my sayings. Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa, ka saurara sosai ga kalmomina.
21 Never lose sight of them; keep them deep within your heart. Kada ka bari su rabu da kai, ka kiyaye su a cikin zuciyarka;
22 For they are life to those who find them, and healing to their whole body. gama rai ne ga waɗanda suke nemansu da kuma lafiya ga dukan jikin mutum.
23 Above all else, guard your heart, for everything you do flows from it. Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka, gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.
24 Keep crooked speech from your mouth, and keep deceitful lips far from you. Ka kau da muguwar magana daga bakinka; ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka.
25 Let your eyes look straight ahead; fix your gaze directly before you. Bari idanunka su dubi gaba sosai, ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.
26 Give careful thought to the path for your feet, and all your ways will be secure. Ka san inda ƙafafunka suke takawa ka bi hanyoyin da suke daram kawai.
27 Do not turn to the right or the left; keep your foot away from evil. Kada ka kauce dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]