Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 My son, do not forget my teaching, but let your heart keep my commandments, Ɗana, kada ka manta da koyarwata, amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,
2 for they will add length of days and years of life and peace to you. gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa su kuma kawo maka wadata.
3 Do not let covenant love and faithfulness leave you; bind them around your neck, write them on the tablet of your heart. Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka.
4 So you will find favor and a good reputation with our Father and with people. Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane.
5 Trust in our Father with all your heart, and do not lean on your own understanding. Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 In all your ways know him, and he will make your paths straight. cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
7 Do not be wise in your own eyes; fear our Father, and turn away from evil. Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
8 This will bring healing to your body and refreshment to your bones. Wannan zai ba wa jikinka lafiya yă kuma adana ƙasusuwanka.
9 Honor our Father with your wealth and with the firstfruits of all your produce, Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
10 then your barns will be filled with plenty, and your vats will overflow with new wine. ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.
11 My son, do not despise the discipline of our Father or be weary of his correction, Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,
12 for our Father disciplines the one his heart loves, just as a father disciplines the son he delights in. domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.
13 Blessed is the one who finds wisdom, and the one who gains understanding, Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, mutumin da ya sami fahimi,
14 for the gain from her is better than gain from silver, and her profit better than gold. gama ta fi azurfa riba tana kuma da amfani fiye da zinariya.
15 She is more precious than jewels, and nothing you desire can compare with her. Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.
16 Long life is in her right hand; in her left hand are riches and honor. Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.
17 Her ways are pleasant, and all her paths are peace. Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi, dukan hanyoyinta kuma salama ne.
18 She is a tree of life to those who take hold of her; those who hold her fast are called blessed. Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta; waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.
19 Our Father by wisdom founded the earth; by understanding he established the heavens; Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya, ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;
20 by his knowledge the depths burst open, and the clouds drop down the dew. ta wurin sani aka rarraba zurfafa, gizagizai kuma suka zubo raɓa.
21 My son, do not lose sight of these; keep sound wisdom and discretion, Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira, kada ka bar su su rabu da kai;
22 and they will be life for your soul and an adornment for your neck. za su zama rai a gare ka, abin adon da zai gyara wuyanka.
23 Then you will walk on your way securely, and your foot will not stumble. Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya, ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;
24 If you lie down, you will not be afraid; when you lie down, your sleep will be sweet. sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba; sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.
25 Do not be afraid of sudden terror, or of the ruin of the wicked when it comes, Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya ko lalacin da yakan auka wa mugaye,
26 for our Father will be your confidence and will keep your foot from being caught. gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.
27 Do not withhold good from those who deserve it, when it is in your power to do it. Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka.
28 Do not say to your neighbor, "Go, and come back, and tomorrow I will give it"—when you have it with you. Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu.
29 Do not plot evil against your neighbor, who lives trustingly beside you. Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, wanda yake zama da aminci kusa da kai.
30 Do not quarrel with anyone for no reason, when he has done you no harm. Kada ka zargi mutum ba dalili, sa’ad da bai yi laifi ba.
31 Do not envy a violent man, and do not choose any of his ways, Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu.
32 for the devious person is detestable to our Father, but he takes the upright into his confidence. Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi.
33 The curse of our Father is on the house of the wicked, but he blesses the home of the righteous. La’anar Ubangiji tana a gidan mugaye, amma yakan albarkaci gidan adali.
34 Toward the mockers he is scornful, but to the humble he gives grace. Yakan yi wa masu girman kai ba’a amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri.
35 The wise will inherit honor, but fools get only disgrace. Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]