Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 My son, if you receive my words and store up my commandments within you, Ɗana, in ka yarda da kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
2 making your ear attentive to wisdom and turning your heart toward understanding; kana kasa kunne ga abin da yake na hikima, kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,
3 yes, if you call out for insight and raise your voice for understanding, in kuma ka kira ga tsinkaya ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,
4 if you seek it like silver and search for it as for hidden treasure, in ka neme shi yadda ake neman azurfa ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,
5 then you will understand the fear of our Father and find the knowledge of our Father. to, za ka gane tsoron Ubangiji ka kuma sami sanin Allah.
6 For our Father gives wisdom; from his mouth come knowledge and understanding. Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
7 He stores up sound wisdom for the upright; he is a shield to those who walk in integrity, Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya, shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
8 guarding the paths of justice and watching over the way of his faithful ones. gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
9 Then you will understand righteousness and justice and fairness—every good path. Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.
10 For wisdom will enter your heart, and knowledge will be pleasant to your soul; Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka, sani kuma zai faranta maka rai.
11 discretion will watch over you, and understanding will guard you, Tsinkaya za tă tsare ka, ganewa kuma za tă yi maka jagora.
12 rescuing you from the way of evil, from men who speak twisted things, Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci,
13 who abandon the paths of uprightness to walk in the ways of darkness, waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,
14 who delight in doing evil and rejoice in the perversity of evil, waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci,
15 whose paths are crooked, and who are devious in their ways. waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu.
16 Wisdom will rescue you also from the forbidden woman, from the stranger with her smooth words, Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,
17 who forsakes the companion of her youth and forgets the covenant of her Father. wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.
18 For her house sinks down to death, and her paths to the dead. Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu.
19 None who go to her return, nor do they reach the paths of life. Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.
20 So you will walk in the way of the good and keep to the paths of the righteous. Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai.
21 For the upright will live in the land, and those of integrity will remain in it; Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar, marasa laifi kuma za su kasance a cikinta;
22 but the wicked will be cut off from the land, and the treacherous will be torn away from it. amma za a fid da mugaye daga ƙasar, za a tumɓuke marasa aminci kuma daga gare ta.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]