Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The proverbs of Solomon, son of David, king of Israel: Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.
2 To know wisdom and instruction, to understand words of insight, Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo; don ganewa kalmomi masu zurfi;
3 to receive instruction in wise conduct, in righteousness, justice, and fairness, don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali, kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;
4 to give prudence to the simple, knowledge and discretion to the young, don sa marar azanci yă yi hankali, yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,
5 let the wise also hear and increase in learning, and let the one who understands gain guidance, bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu, bari masu tunani kuma su sami jagora,
6 to understand a proverb and a parable, the words of the wise and their riddles. don su fahimci karin magana da kuma misalai, kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.
7 The fear of our Father is the beginning of knowledge; fools despise wisdom and instruction. Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da horo.
8 Listen, my son, to your father's instruction, and don't turn away from your mother's teaching, Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
9 for they are a graceful garland for your head and pendants for your neck. Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
10 My son, if sinners entice you, do not give in. Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.
11 If they say, "Come with us, let us lie in wait for blood, let us ambush the innocent without cause; In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;
12 like the grave let us swallow them alive, and whole, like those who go down to the pit; mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
13 we will find all kinds of precious goods, we will fill our houses with plunder; za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;
14 throw in your lot with us; we will all share one purse," ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”
15 my son, do not walk in the way with them; hold back your foot from their paths, ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;
16 for their feet run to evil, and they hurry to shed blood. gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai.
17 For a net spread out before any bird's eyes catches nothing; Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye!
18 but these lie in wait for their own blood; they ambush their own lives. Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko; ba sa kama kome, sai rayukansu!
19 Such are the ways of everyone greedy for unjust gain; it takes away the life of its possessors. Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau; ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu.
20 Wisdom cries aloud in the street; in the open squares she lifts her voice. Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi, tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;
21 At the head of the noisy streets she calls out; at the entrance of the city gates she speaks: tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu, tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.
22 "How long, simple ones, will you love being simple? How long will mockers delight in their mocking and fools hate knowledge? “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi?
23 If you respond to my correction, I, Wisdom, will pour out my spirit on you; I will make my words known to you. Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina.
24 Because I have called and you refused, I stretched out my hand and no one paid attention, Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,
25 and you ignored all my counsel and rejected all my correction, da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,
26 I also will laugh at your calamity; I will mock when terror overtakes you, Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,
27 when terror overtakes you like a storm and your calamity comes like a whirlwind, when distress and anguish come upon you. sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.
28 Then they will call on me, but I will not answer; they will seek me earnestly but will not find me, “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.
29 because they hated knowledge and did not choose the fear of our Father, Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,
30 they rejected my counsel and despised all my correction. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,
31 So they will eat the fruit of their own way and have their fill of their own schemes. za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.
32 For the waywardness of the simple will kill them, and the complacency of fools will destroy them; Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;
33 but whoever listens to me will dwell secure and be at ease, without dread of disaster." amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]