Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 19 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Better is a poor person who walks in his integrity than one whose words are crooked and is a fool. Gara matalauci wanda yake marar laifi da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.
2 Also, desire without knowledge is not good, and whoever acts in haste misses the way. Ba shi da kyau ka kasance da niyya babu sani, ko ka kasance mai garaje ka ɓace hanya.
3 A person's own foolishness ruins his way, yet his heart rages against our Father. Wautar mutum kan lalatar da ransa, duk da haka zuciyarsa kan ba wa Ubangiji laifi.
4 Wealth adds many friends, but the poor is separated from his friend. Wadata kan kawo abokai da yawa, amma abokin matalauci kan bar shi.
5 A false witness will not go unpunished, and one who breathes out lies will not escape. Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.
6 Many seek the favor of a generous person, and everyone is a friend to one who gives gifts. Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki, kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne.
7 All the brothers of a poor person hate him; how much more do his friends keep far from him! He calls after them, but they are gone. ’Yan’uwan matalauci sukan guje shi, balle abokansa, su ma za su guje shi. Ko da yake matalaucin yana binsu yana roƙo, ba zai sam su ba.
8 Whoever gets wisdom loves his own soul; whoever guards understanding will find good. Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa; duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba.
9 A false witness will not go unpunished, and one who breathes out lies will perish. Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka.
10 Luxury is not fitting for a fool—much less for a servant to rule over princes. Bai dace da wawa ya yi rayuwa cikin jin daɗi ba, haka ya fi muni bawa ya yi mulki a kan sarki!
11 The good sense of a person makes him slow to anger, and it is his glory to overlook an offense. Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.
12 A king's wrath is like the roaring of a lion, but his favor is like dew on the grass. Fushin sarki yana kama da rurin zaki, amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa.
13 A foolish son is ruin to his father, and a wife's quarreling is a continual dripping. Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne, mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.
14 House and wealth are an inheritance from one's ancestors, but a prudent wife is from our Father. Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne, amma mace mai basira daga Ubangiji ne.
15 Laziness casts into deep sleep, and an idle person will go hungry. Ragwanci kan jawo zurfin barci, mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.
16 Whoever keeps the commandment keeps his life; whoever despises his ways will die. Duk wanda ya bi umarnai kan tsare ransa, amma duk wanda ya ƙi binsu zai mutu.
17 Whoever is generous to the poor lends to our Father, and our Father will repay him for his deed. Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne, zai kuwa sami lada game da abin da ya yi.
18 Discipline your son while there is hope, and do not set your heart on his destruction. Ka hori ɗanka, gama yin haka akwai sa zuciya; kada ka goyi baya lalacewarsa.
19 A person of great wrath must pay the penalty; for if you rescue him, you will only have to do it again. Dole mai zafin rai yă biya tara; in ka fisshe shi sau ɗaya, to, sai ka sāke yin haka.
20 Listen to counsel and accept discipline, that you may gain wisdom in the days to come. Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni, a ƙarshe kuwa za ka yi hikima.
21 Many are the plans in a person's heart, but it is the counsel of our Father that will stand. Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum, amma manufar Ubangiji ce takan cika.
22 What is desired in a person is covenant love, and a poor person is better than a liar. Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa; gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci.
23 The fear of our Father leads to life, and whoever has it rests satisfied, untouched by harm. Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai. Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi.
24 The sluggard buries his hand in the dish and will not even bring it back to his mouth. Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa!
25 Strike a mocker, and the simple will learn prudence; reprove a person of understanding, and he will gain knowledge. Ka bulale mai ba’a, marasa azanci kuwa za su yi la’akari; ka tsawata wa mai basira, zai kuwa ƙara sani.
26 Whoever does violence to his father and drives away his mother is a son who brings shame and disgrace. Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci.
27 Stop listening to instruction, my son, and you will stray from the words of knowledge. In ka daina jin umarni, ɗana, za ka kuwa kauce daga kalmomin sani.
28 A worthless witness mocks at justice, and the mouth of the wicked gulps down wickedness. Mai shaidar da yake malalaci yana wa shari’a ba’a ne, bakin mugaye kuma na haɗiye mugunta.
29 Punishment is prepared for mockers, and beatings for the backs of fools. An shirya tara saboda masu ba’a ne, dūka kuma saboda bayan wawaye.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]