Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 20 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Wine is a mocker, strong drink a brawler, and whoever staggers under it is not wise. Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne; duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.
2 The terror of a king is like the growl of a lion; whoever provokes him to anger forfeits his own life. Fushin sarki yana kama da rurin zaki; duk wanda ya sa shi fushi zai rasa ransa.
3 It is an honor for a person to keep clear of strife, but every fool is quick to quarrel. Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.
4 A lazy person will not plow in autumn; so at harvest he looks for a crop and finds nothing. Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.
5 The purposes of a person's heart are deep waters, but one who has understanding draws them out. Manufofin zuciyar mutum zurfafan ruwaye ne, amma mutum mai basira yakan jawo su.
6 Many a person proclaims his own loyal love, but a faithful one—who can find? Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne, amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda.
7 The righteous walk in their integrity; blessed are their children after them! Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi; masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa.
8 A king seated on the throne of judgment winnows out all evil with his eyes. Sa’ad da sarki ya zauna kan kujerarsa don yă yi shari’a, yakan ga dukan mugunta da idanunsa.
9 Who can say, "I have kept my heart pure; I am cleansed from my sin"? Wa zai iya cewa, “Na kiyaye zuciyata da tsarki; ni mai tsabta ne marar zunubi kuma”?
10 Unequal weights and unequal measures—our Father detests them both. Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba, Ubangiji ya ƙi su duka.
11 Even a child is known by his actions, by whether his conduct is pure and upright. Akan san ƙananan yara ta ayyukansu, ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta.
12 The hearing ear and the seeing eye—our Father made them both. Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani, Ubangiji ne ya yi su duka.
13 Do not love sleep, or you will grow poor; open your eyes, and you will have plenty of bread. Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.
14 "Worthless, worthless!" says the buyer—then off he goes and boasts of his bargain. “Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya; sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki.
15 There is gold and an abundance of jewels, but lips that speak knowledge are a rare treasure. Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace, amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja.
16 Take the garment of one who puts up security for a stranger; hold it as a pledge when he does so for foreigners. A karɓi rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
17 Bread gained by deceit tastes sweet, but afterward the mouth is full of gravel. Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi, amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi.
18 Plans are established by counsel; so wage war only with wise guidance. Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara; in kana yaƙi, ka sami bishewa.
19 A gossip betrays a confidence; so do not keep company with a babbler. Mai gulma yakan lalace yarda; saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu.
20 Whoever curses his father or mother—his lamp will be snuffed out in deepest darkness. In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, fitilarsa za tă mutu a tsakiyar duhu.
21 An inheritance gained too quickly at the start will not be blessed in the end. Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba.
22 Do not say, "I will pay back evil for evil." Wait for our Father, and he will deliver you. Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!” Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka.
23 Our Father detests unequal weights, and dishonest scales are no good. Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba, da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.
24 A person's steps are directed by our Father; how then can anyone understand his own way? Ubangiji ne yake bi da matakan mutum, Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa?
25 It is a trap to rashly dedicate something and only later reconsider the vow. Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.
26 A wise king winnows out the wicked and drives the threshing wheel over them. Sarki mai hikima yakan gane mugunta; ya hukunta su ba tausayi.
27 The human spirit is the lamp of our Father, searching every inmost part. Fitilar Ubangiji kan bincika zuciyar mutum takan bincika lamirinsa.
28 Loyal love and faithfulness preserve a king; by loyal love his throne is upheld. Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya; ta wurin ƙauna sarautarsa za tă zauna a kafe.
29 The glory of the young is their strength, but the splendor of the old is gray hair. Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu, furfura ita ce darajar tsofaffi.
30 Wounding blows scrub away evil, and beatings cleanse the inmost parts. Naushi da rauni kan share mugunta, dūka kuma kan tsabtacce lamiri.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]