Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 21 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The king's heart is a stream of water in our Father's hand; he turns it wherever he pleases. A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne wanda yake bi da shi duk inda ya so.
2 Every way of a person seems right in their own eyes, but our Father weighs the heart. Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke, amma Ubangiji yakan auna zuciya.
3 To do what is right and just is more pleasing to our Father than sacrifice. Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.
4 Haughty eyes and a proud heart—the lamp of the wicked—are sin. Girmankai da fariya, su ne fitilar mugaye, wannan kuwa zunubi ne!
5 The plans of the diligent lead surely to abundance, but all who are hasty end up in poverty. Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci.
6 Making a fortune by a lying tongue is a fleeting vapor, a deadly trap. Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya tarin tururi ne da kuma mugun tarko.
7 The violence of the wicked will drag them away, because they refuse to do what is just. Rikicin mugaye zai yi gāba da su, gama sun ƙi su yi abin da yake daidai.
8 The way of the guilty is crooked, but the conduct of the pure is upright. Hanyar mai laifi karkatacciya ce, amma halin marar laifi sukan aikata gaskiya.
9 Better to live in a corner of the roof than in a shared house with a quarrelsome wife. Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
10 The soul of the wicked craves evil; their neighbor finds no mercy in their eyes. Mugun mutum yakan zaƙu ya aikata mugunta; maƙwabcinsa ba ya samun jinƙai daga gare shi.
11 When a mocker is punished, the simple grow wise; when the wise are instructed, they gain knowledge. Sa’ad da aka hukunta mai ba’a marasa azanci suka yi wayo; sa’ad da aka yi wa mai hikima umarni yakan sami sani.
12 Our Father, the Righteous One, observes the house of the wicked and brings the wicked to ruin. Mai Adalci kan lura da gidan mugu kan kuma zama sanadin lalacin mugu.
13 Whoever shuts their ears to the cry of the poor will also cry out and not be answered. In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba.
14 A gift given in secret soothes anger, and a bribe slipped into the cloak calms strong wrath. Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi, kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani.
15 When justice is done, it is a joy to the righteous but terror to those who do evil. Sa’ad da aka yi adalci, yakan kawo farin ciki ga mai adalci amma fargaba ga masu aikata mugunta.
16 A person who strays from the way of understanding will rest in the assembly of the dead. Mutumin da ya kauce daga hanyar fahimi kan zo ga hutu a ƙungiyar matattu.
17 Whoever loves pleasure will become poor; whoever loves wine and oil will never grow rich. Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci; duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba.
18 The wicked become a ransom for the righteous, and the treacherous for the upright. Mugu kan zama abin fansa don adali, marar aminci kuma don mai aikata gaskiya.
19 Better to live in a desert land than with a quarrelsome and complaining wife. Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali.
20 Precious treasure and oil are in the home of the wise, but a fool devours all he has. A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau, amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.
21 Whoever pursues righteousness and faithful love will find life, righteousness, and honor. Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna kan sami rai, wadata da girmamawa.
22 A wise person scales the city of the mighty and brings down the stronghold they trust in. Mutum mai hikima kan fāɗa wa birnin jarumawa ya kuma rushe katangar da suka dogara a kai.
23 Whoever guards their mouth and tongue keeps themselves out of trouble. Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa.
24 "Mocker" is the name of the proud and arrogant who acts with outrageous insolence. Mai girmankai da kuma mai fariya, “Mai ba’a” ne sunansa; yana yin abubuwa da girmankai ainun.
25 The craving of a lazy person kills him, for his hands refuse to work. Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.
26 All day long the craving grows, but the righteous give and do not hold back. Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake.
27 The sacrifice of the wicked is detestable—how much more when brought with evil intent. Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi!
28 A false witness will perish, but whoever listens will testify with lasting effect. Mai ba da shaidar ƙarya zai hallaka, kuma duk wanda ya saurare shi zai hallaka har abada.
29 The wicked put on a bold face, but the upright give thought to their ways. Mugun mutum kan yi tsayin daka, amma mai aikata gaskiya kan yi tunani a kan abin da yake yi.
30 There is no wisdom, no understanding, no counsel that can stand against our Father. Babu hikima, babu tunani, babu shirin da zai yi nasara a kan Ubangiji.
31 The horse is made ready for the day of battle, but victory belongs to our Father. Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]