Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Proverbs 22 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 A good name is to be chosen rather than great riches, and favor is better than silver or gold. An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa; tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.
2 The rich and the poor meet together; our Father is the Maker of them all. Mawadaci da matalauci suna da abu guda. Ubangiji ne Mahaliccinsu duka.
3 The prudent sees danger and takes cover, but the simple keep going and pay the price. Mai basira kan ga damuwa tana zuwa yă nemi mafaka, amma marar azanci kan yi ta tafiya yă kuma sha wahala.
4 The reward for humility and the fear of our Father is riches and honor and life. Sauƙinkai da tsoron Ubangiji sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.
5 Thorns and snares lie in the path of the crooked; whoever guards his soul stays far from them. A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko, amma duk wanda ya kiyaye ransa kan kauce musu.
6 Train up a child in the way he should go, and even when he is old he will not depart from it. Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi, kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
7 The rich rules over the poor, and the borrower is slave to the lender. Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.
8 Whoever sows injustice will reap calamity, and the rod of his fury will fail. Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala, za a kuma hallaka sandar fushinsa.
9 Whoever has a generous eye will be blessed, for he shares his bread with the poor. Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta.
10 Drive out the scoffer, and strife goes with him; quarreling and abuse will cease. Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje; fitina da zargi kuma za su ƙare.
11 Whoever loves a pure heart and speaks graciously will have the king as his friend. Duk mai son tsabtar zuciya wanda kuma jawabinsa mai alheri ne zai zama aminin sarki.
12 The eyes of our Father keep watch over knowledge, but he overturns the words of the traitor. Idanun Ubangiji na lura da sani, amma yakan ƙi kalmomin marar aminci.
13 The lazy person says, "There is a lion outside! I will be killed in the streets!" Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!” Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”
14 The mouth of forbidden women is a deep pit; whoever draws our Father's anger will fall into it. Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi; duk wanda yake a ƙarƙashin fushin Ubangiji zai fāɗa a ciki.
15 Foolishness is bound up in the heart of a child, but the rod of discipline drives it far away. Wauta tana da yawa a zuciyar yara, amma sandar horo zai kore ta nesa da su.
16 Whoever oppresses the poor to enrich himself, or gives to the rich, will come only to poverty. Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.
17 Listen carefully to the words of the wise, and apply your heart to my knowledge, Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima; ka yi amfani da abin da nake koyarwa,
18 for it will be pleasant if you keep them within you, if all of them are ready on your lips. gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka ka kuma kasance da su a shirye a leɓunanka.
19 So that your trust may be in our Father, I have made them known to you today, even to you. Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji, ina koya maka yau, har kai ma.
20 Have I not written for you thirty sayings of counsel and knowledge, Ban rubuta maka maganganu talatin ba, maganganun shawara da sani,
21 to teach you what is right and true, so that you may give a true answer to those who sent you? ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai, saboda ka iya ba da amsa daidai ga duk wanda ya aike ka?
22 Do not rob the poor because he is poor, or crush the afflicted at the gate, Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a,
23 for our Father will plead their cause and will rob of life those who rob them. gama Ubangiji zai yi magana dominsu zai kuwa washe waɗanda suka washe su.
24 Do not befriend a man given to anger, and do not go with a hot-tempered man, Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,
25 or you will learn his ways and entangle yourself in a snare. in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko.
26 Do not be one of those who give pledges, who put up security for debts. Kada ka zama mai ɗaukar lamuni ko ka ba da jingina saboda bashi;
27 If you have nothing to pay with, why should your bed be taken from under you? gama in ka kāsa biya za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.
28 Do not move the ancient boundary stone that your fathers set up. Kada ka matsar da shaidar kan iyakar da kakanninka suka kafa.
29 Do you see a man skillful in his work? He will stand before kings; he will not stand before ordinary men. Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa? Zai yi wa sarakuna hidima; ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]